A Najeriya, wa su gwamnoni a yankin arewa maso yammacin kasar sun sha alwashin ci gaba da hada kai a tsakanin su don ganin an magance matsalar sace sacen shanu a jihohin su.
Akan haka ne gwamnonin jihohin shida da ke shiyyar suka gudanar da wani taro a Kaduna da nufin tsara yadda za'a magance matsalar tsaro musamman satar shanu a Dajin Kamuku mai makwabtaka da akasarin jihohin.
Rahotanni sun ce kimanin kananan hukumomi tara ne a jihohin ke fama da hare hare barayin shanu daga Dajin na Kamuku, lamarin daya tagayyara mutane da dama a jihohin.
A tattaunawar sa da BBC gwamnan jahar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya ce gwamnatin jahar Katsina za ta ci gaba da hada gwiwa da sauran jihohin har sai an ga bayan irin wadannan bata gari. Source: BBC Hausa
Comments
Post a Comment